<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><hymn_number>119</hymn_number>
<title>Zo, Mutane, Rera Waƙa LW119</title>
<lyrics>[V1]
 1) Zo, mutane, rera waƙa,
 Cika sammai da yabo.
 Yabe shi, Mai Magani ne,
 Don ya ceci duniya.
 Makiyayi, Mai Cetonmu,
 Ana biyayya da shi.

[V2]
 2) Saboda cetonmu ne fa,
 Ya zo ya ba da jininsa,
 Ya yi aikin gafara ma,
 Ya mutu, mun huta ma.
 Tashinsa na ɗaukaka ne,
 Sarkin rai har abada.

[V3]
 3) Yanzu bisa kursiyinsa
 Girma, iko nasa ne.
 Ana rera, Halleluya,
 Waƙar ƴaƴan haske ce,
 Shi Sarki nc da Shugaba,
 Nasara duk tasa ce.

[V4]
 4) Ga giraya da algaita,
 Rera waƙar yabonsa.
 Duniya ma ki saurare mu,
 Sarkin rai ya rinjaya!
 Rago wanda aka kashe
 Ya rayu, ya tashi kuwa.

[V5]
 5) Yabo, ɗaukaka ga Uba,
 Yabo, ɗaukaka ga Ɗa,
 Yabo, ɗaukaka ga Ruhu,
 Uku cikin ɗaya ne.
 Makaɗaicin Allah namu
 Girma, yabo nasa ne.</lyrics>
</song>